ABNA24 : Sojojin na Faransa dai suna yankin ne tun shekara ta 2013 suna gudanar da ayyukan hare-hare a ƙasashen Mali, Chadi, Nijar, Burkina Faso da kuma Mauritaniya.
Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo ra’ayin wasu daga cikin ‘yan ƙasar kan wannan mataki na Faransa inda suka nuna farin cikinsu kan hakan.
Wani ɗan kasuwa mai sai da wayoyi, mai suna Samba Diakite, da kafar ta yi hira da shi ya bayyana cewar: Barin rabin sojojin Faransa ƙasar Mali wani lamari ne mai kyaun gaske. Yana mai cewa idan suka bar ƙasar wataƙila za a samu wasu da suke da kyakkayawar niyyar taimakon mu su zo su taimaka.
Da dama daga cikin ‘yan ƙasar Mali ɗin dai suna ganin zaman sojojin Faransan tamkar wani ci gaba ne da mulkin mallakar da ta yi wa ƙasar wanda kuma ba a shirye suke su ci gaba da amincewa da shi ba.
A jiya Juma’a ce dai shugaban ƙasar Faransan Emmanuel Macron ya sanar da rage sojojin Faransa a yankin na Sahel inda ya ce sojojin da za’a ragen dai sun haɗa da waɗanda suke aikin ‘tabbatar da tsaro’ a arewacin ƙasar Mali’da suka haɗa da na sansanonin sojojin Faransa a Timboktu, Kidal da kuma Tessalit.
342/